6 Satumba 2024 - 17:51
Al-Qassam Ta Wallafa Faifan Bidiyon Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi Na Karshe Daga Cikin Mutane Shida Da Aka Kashe Fursunonin Sahyoniyawan

Bataliyar shahidi Ezzuddin Al-Qassam reshen soja na Hamas ta fitar da wani faifan bidiyo na fursinoni na karshe na gungun fursinonin yahudawan sahyoniya 6 wadanda a baya-bayan nan gwamnatin sahyoniyawa ta yi ikirarin dawo da gawarwakinsu daga Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, a cikin wannan faifan bidiyo Al-Moj Sarousi fursunan yhaudawan ya bayyana cewa: Majalisar ministocin kasar Isra'ila da sojojinta da kuma hukumomin leken asiri sun kasa cimma nasarar kubutar da fursunoni a harin da aka kai a Gaza wanda shi ya sa aka kashe su

Sarousi mai shekaru 27 ya kara da cewa shi da sauran fursunonin yahudawan sahyoniya da ke Gaza su ne hadafin hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaiwa.

Wannan fursunan yahudawan sahyoniya ya bukaci a sako dukkan fursunonin "ba tare da rasa gashin kansu ko daya ba".

Sarousi ya dauki cewa majalisar ministocin Benjamin Netanyahu, da sojoji da sauran hukumomin tsaro na gwamnatin sahyoniyawa ne ke da alhakin kama shi da mukarrabansa a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2017.

Yayin da yake ishara da mawuyacin halin da fursunonin ke fuskanta a Gaza, fursunan yahudawan sahyoniya da aka kashe ya ce: Ba mu da ruwa, wutar lantarki ko abinci kun kyalemu mu. Domin mun nemi taimakon ku. Amma a martani ka bayyana cewa “ku taimaki kanku da kanku kuma ba wanda zai iya cetonku wannan lamarin kuwa shi ya kai ga kama mu.

A ƙarshe, Mouj Sarosi ya yi wa iyalinsa jawabi ya ce: Ku yi ta zanga-zanga Domin ku ne fatanmu kuma mun aminta da ku.

Rundunar shahid Ezzuddin Al-Qassam ta fara yada sakonnin karshe na fursunonin Isra’ila shida da aka kashe a Gaza tun ranar litinin da ta gabata. Fursunonin sun dorawa majalisar ministocin gwamnatin Sahayoniya karkashin jagorancin Benjamin Netanyahu da jami'an tsaro da na soja na wannan gwamnatin a matsayin alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Fursunonin sun kuma bukaci da a gaggauta cimma yarjejeniyar sakin fursunonin da kuma ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman a dawo da fursunonin kafin a kashe su.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai rundunar Al-Qassam suka buga wani sako ga ra'ayin al'ummar yahudawan sahyoniya, inda a ciki aka bayyana cewa: Maimakon mayar da fursunonin ku, Netanyahu ya zabi ya ci gaba da kula da yankin Philadelphia.

Wannan kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta jaddada cewa: Wadannan fursunoni suna raye. Amma sun shiga tarihi. Netanyahu ya bar dubban "Ron Arad" ga Isra'ila.

"Ron Arad" matukin jirgin Isra'ila ne wanda jirginsa ya yi hadari a kudancin kasar Lebanon a watan Oktoban shekarar 1986 (1365) kuma har yanzu ba a san makomarsa ba.

Abu Ubaidah, kakakin bataliyoyin al-Qassam, ya sanar a ranar 23 ga Afrilu (4 Ardibehesht) cewa yanayin da Ron Arad ya kasance shi ne mafi kusantar yanayin fursunonin makiya a Gaza.

Abu Ubaidah ya kara da cewa: "Matsi na soji" riyawa ne kawai ba zai haifar da wani sakamako ba face tabbatuwa da dakewarmu a wurarenmu da kuma kiyaye hakkokin al'ummar Palastinu da kuma rashin yin kasa a gwiwa a kai.